NASIHA
-HIKIMA KAYAN MUMINAI. -Masu Hikima Suna Cewa: "Ka Zamo Ƙofa Wacce Alkhairai Zasu Riƙa Shigowa ta Cikinta, idan Ba Zaka iya Hakan Ba to ka Zamo Tamkar Taga Wacce Haske Zai Riƙa Shigowa ta Ciki, idan Ba za ka iya Haka Ba to ka Zamo Katanga Wacce Mutane Masu Rauni Zasu Riƙa Jingina da lta". -Haƙuri iri Biyu Ne: Haƙuri Akan Abin da Kake So idan Ba ka Same Shi Ba, da Kuma Haƙuri Akan Abin da Baka So idan Ya Same Ka. -Duk Ƙofar da Ka Ganta A Rufe Tana da Mabuɗi, Kada Ka Saki Baki Kana Jiranta ta Buɗe da Kanta. -Duk Wanda Ya Zagi Wani Tare da Kai Wata Rana Sai Ya Zage ka Tare da Wani. -Komai A Duniya Yana da Mabuɗi: Mabuɗin ilimi Shine Tambaya, Mabuɗin Nasara Kuma Hakuri, Mabuɗin Arziki Tsoron Allah, Mabuɗin Zaman Lafiya Kuma Adalci da Gaskiya. -Kuyi Hattara da Mabuɗai Guda Uku: (1)-Fushi, Mabuɗin Azaba. (2)-Tsoro, Mabuɗin Ƙasƙanci da Fitina. (3)-Kwaɗayi Kuma Mabudin Wahala. -Ba Zaka Taɓa Sauƙa A Tashar Nasara Ba Sai Dai idan ka Hau Motar Haƙuri da Ƙoƙari da Sadaukarw...