NASIHA

 -HIKIMA KAYAN MUMINAI.




-Masu Hikima Suna Cewa: 

"Ka Zamo Ƙofa Wacce Alkhairai Zasu Riƙa Shigowa ta Cikinta, idan Ba Zaka iya Hakan Ba to ka Zamo Tamkar Taga Wacce Haske Zai Riƙa Shigowa ta Ciki, idan Ba za ka iya Haka Ba to ka Zamo Katanga Wacce Mutane Masu Rauni Zasu Riƙa Jingina da lta".


-Haƙuri iri Biyu Ne: 

Haƙuri Akan Abin da Kake So idan Ba ka Same Shi Ba, da Kuma Haƙuri Akan Abin da Baka So idan Ya Same Ka.


-Duk Ƙofar da Ka Ganta A Rufe Tana da Mabuɗi, Kada Ka Saki Baki Kana Jiranta ta Buɗe da Kanta.


-Duk Wanda Ya Zagi Wani Tare da Kai Wata Rana Sai Ya Zage ka Tare da Wani.


-Komai A Duniya Yana da Mabuɗi:

 Mabuɗin ilimi Shine Tambaya, Mabuɗin Nasara Kuma Hakuri, Mabuɗin Arziki Tsoron Allah, Mabuɗin Zaman Lafiya Kuma Adalci da Gaskiya.


-Kuyi Hattara da Mabuɗai Guda Uku:

(1)-Fushi, Mabuɗin Azaba.

(2)-Tsoro, Mabuɗin Ƙasƙanci da Fitina.

(3)-Kwaɗayi Kuma Mabudin Wahala.


-Ba Zaka Taɓa Sauƙa A Tashar Nasara Ba Sai Dai idan ka Hau Motar Haƙuri da Ƙoƙari da Sadaukarwa.


-Zuciyar ka Itace Adireshin Ka, Harshenka Shine Ma'auninka, Gyara Harshen ka Sannan Ka Kula da Ayyukanka.


-Kada Ka Damu da Masu Kulla Maka Sharri, Duk iya Ƙokarinsu Basu Wuce 'Ƴan sa ido Ga Abin da Allah Ya Hukunta  Maka Ba.


-Mutane Iri Uku Ne: 

(1)-Wasu Kamar Guba Suke Kullum Gudunsu Ake yi.

(2)-Wasu Kuma Kamar Magani Suke Kullum Akai-Akai ake Buƙatarsu.

(3)-Wasu Kuma Kamar Abinci Suke A Kullum Dole Sai An Nemesu, Yi Ƙoƙari Ka Zama Wanda A Kullum ake Nemansa Saboda Amfaninsa.


-Malam! Duk Yadda Kayi Sai Wani Ya Zage Ka, Ka Manta Da Mutane Kayi Komai Yadda Ya Kamata Domin Neman Yardar Allah Ta'ala.


-Kada Ka Cuci Wanda Ya Cuce Ka, Shi Sharri Kare Ne, Ko Yayi Nisa Sai Ya Dawowa Mai Shi.


-Duk Abinda Kayi Na Alkhairi Masoyanka Kawai Kake Burgewa, Su Masassada Sai dai Su yi Murmushi Don Su Ɓatar da Hankalinka, Amma Fa Hassada ga Mai Rabo Taki Ce.


-Ka Zamo Mai Haƙuri da Bada Uziri ga Wanda Yayi Maka Ba Dai-Dai Ba, Kada Ka Damu da Mai Ƙin Ka Ko Wanda Yake Sukar Ka; Rufin Asirin da Allah Yayi Maka Ne Ya Janyo Maka.


-Ka ji Tsoran Allah Sai Ya Taimake ka, Kayi Ma'amala da Kowa Bisa Kyautatawa Sai Kayi Nasara. 


           ☆via-the2brothers-links☆


Comments

Popular posts from this blog

Dararen Lailatul Qadri:

£îd Mûbãräk

Taskar Ahlul Baitin-Nabiy (s).