Taskar Ahlul Baitin-Nabiy (s).
☆via-the2brothers-links☆
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Ka tsare harshenka kamar yadda kake tsare dukiyarka. Domin sau da yawa wata maganar tana kore alheri. Wata maganar kuma tana janyo sharri".
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Babbar hanyar zama lafiya itace sallamawa ga iko da kaddarar ubangiji".
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Jure masifa jarumta ce kamun kai arzikine. Tsare kai daga sabon Allah shine babbar garkuwa".
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Talauci yana nakasa hujjar ma'abocin hankali. Talaka yakan zama bako a garin haihuwarsa."
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Kada kaji kunya ko nauyin bayar da kadan. Domin hana kadan din yafi bayar da kadan din karanta.
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Mai aikata kyakkyawan aiki yafi kyakkyawan aikin kyau kamar yadda mai aikata mummunan aiki yafi mummunan aikin muni".
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Lafiyar jikinka tana karuwa idan hassadarka tana raguwa".
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Zunubi mai hadari shine wanda mai aikatashi ya dauke shi karami".
Imam Ali (A.S) Yana cewa:
"Dangantaka tana bukatar kauna fiye da yadda kauna take bukatar dangantaka".
☆via-the2brothers-link☆
Comments
Post a Comment