Taskar Ahlul Baitin-Nabiy (s).

     ☆via-the2brothers-links☆

 Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.


-HADISAI GOMA DAGA IMAM BAQIR (AS):


1- Imam Baqir (AS) Yace: 

"Farkon Abin da Za'a Yiwa Bawa Hisabi Dashi Itace Sallah, Idan ta Ƙarɓu to Dukkan Sauran Ayyukan Bawa Za'a Karbe su.

- Bihar 7/267.


2- Imam Baqir (AS) Yace:

 "Hadisan mu (Maganganunmu) Suna Raya Zukata Ne".

- Bihar 2/144.


3- Imam Baqir (AS) Yace: 

"Duk Wanda Ya Kasance Mai Biyayya ga Allah (T) to shi Masoyinmu Ne. Hakanan Kuma Wanda Ya Kasance Mai Saɓawa Allah to Shi Maƙiyinmu Ne."

- Alkafiy 2/75.


4- Imam Baqir (AS) Yace: 

"Ku Nemi ilimi, Domin Nemansa Abu ne Mai Kyau Kuma Koyonsa Ibada Ce."

- Biharul Anwar 74/189.


5- Imam Baqir (AS) Yace:

 "Me Tuba Daga Zunubai Kamar Wanda Bashi da Zunubai Ne Kwata-Kwata"

- Wasa'il 16/74.


6- Imam Baqir (AS) Yace:

 "Ya Wajaba ga Mumini Akan Ɗan Uwansa Mumini Ya Ɓoye (Sirranta) Masa Manya Manyan Zunubansa Guda Saba'in (70) Daga Sanin Mutane."

- Bihar 74/301.


7- Imam Baqir (AS) yace: 

"Ba Wani Mutum da Zai Kuɓuta Daga Zunubansa har Sai Ya Kiyaye Harshensa."

- Bihar 78/178.


8- Imam Sadiq (AS) Yace:

 "Wata Mata Tazo Wajen Manzon Allah (S) ta Tambaye Shi; Ya Ma'aikin Allah Menene Haƙƙin Miji Akan Matarsa? Sai Manzon Allah (S) Yace Mata: 'Haƙƙin Miji Akan Matarsa Shine ta bi Umurninsa Kar ta Saɓa Masa."

- Wasa'il 10/527.


9- Imam Baqir (AS) Yace: 

"Manzon Allah (S) Ya La'anci Mutumin da Yake Kallon Farjin Matan da ba Tasa Ba, da Mutumin da Yake Ha'intar Ɗan'uwansa Musulmi Akan Matarsa, da Kuma Mutumin da Mutane Ke Buƙatar Taimako A Wajensa Amma Yake Ƙarban Cin Hanci A Wajensu Kafin Ya Taimaka Musu."

- Al-Kafiy 5/559.


10- Imam Baqir (AS) Yace:

 "Babu Wata ibada da Tafi Falala A Wajen Allah (T) Fiye da Kame Ciki Daga Haram da Kame Farji Daga Zina.

- Alkafiy 2/80.


          ☆via-the2brothers-links☆


Comments

Popular posts from this blog

Dararen Lailatul Qadri:

£îd Mûbãräk

Keyboard Shortcut