Dararen Lailatul Qadri:
Alhamdulillah yau Allah ya kawo mu dare na farko (cikin dararen lailatul Qadri) a wannan wata mai tarin Albarka.
LAILATUL KADARI YA FI DARE DUBU (1000)
A cikin watan (Ramadan) akwai wani dare ya fi dare 1000. Wato ka samu ka yi ibada a cikinsa ya fi ka yi dare dubu kana ibada kenan. Wato kimanin shekaru kusan 100, wajen tis'in da nawa kenan? An ce 'Khairun' ne, ba a ce daidai wadaida ba.
اللهم صل على محمد وآل محمد
وعجل فرجهم📿
SALLAR DAREN SHA TARA GA WATAN RAMADAN, DAREN LAILATUL QADRI.
Yau Alhamis18 ga Watan Ramadan dare na Farko daga cikin dararen lailatul Qadri Wato Daren 19,21,23, Wadan nan Sune dare na lailatul Qadri .
AYYUKAN DAREN YAU 19 GA WATAN RAMADAN
1. Anaso ayi Wanka irin na ibada a Daren Yau, Kuma Anfiso Ayishi a Farkon Daren.
2. Karanta Ziyarar Imam Hussain (As) Tana daga cikin Ayyuka mafi girma a wannan dare.
3. Tsinewa Makashin Wasiyin Manzon Allah (Imam Ali As) sau 100 "Allahumma la'an Man Qatala Amirul Muminin kafa 100.
4. Tunawa da Kisan da aka yi wa Imam Ali (As)
5. Karanta Du'aul Jaushanil Kabir Mai dauke Sunan Allah 1000.
6. Karanta Du'aul Khumail
7. Karanta Inna Anzalnahu Kafa 1000
8,Karanta Astagfirullaha rabbi wa atubu ilaihi kafa 100.
9. Akwai A'amal din da ake Daura Alkur'ani akai ,Yayin da ake karanta adduar Ana Tawassuli da Allah da Manzo Tare da Iyalan gidan sa.
10. Sallah mai raka'a 50 Fatiha da Izazul a kowace raka'a
11. Sallah mai raka'a 2 Fatiha da Kulhuwallahu 7 a kowace raka'a, Bayan Sallama sai a karanta "Astagfirullaha Rabbi wa atubu ilaihi kafa 70 .
12. Sallah mai raka'a 100 Sallama 50 Fatiha da Kulhuwallahu 10 a kowace raka'a, Akwai Falala mai Yawan Gaske.
Yazo a ruwaya cewa duk wani Wanda yayi wannan Sallar bazai tashi daga inda yayi Sallar ba har sai Allah ya gafarta masa Zunubansa Tare dana Iyayansa ,Sannan Allah zai aiko da wasu Mala'iku Wanda zasu Rubuta masa lada har Shekara mai zuwa,Kuma za a sa wasu daga cikin Mala'iku Suyita Gina masa Hamshakin gida a cikin Aljannah tare da 'dasa masa Bishiyoyi a cikin gidan Aljannah, Duk wanda yayi wannan bazai bar Duniya ba har sai Allah ya nuna masa duk wadannan abubuwan.
Allah yasa muna cikin wadan da zasu samu duk Alkhairan dake cikin wannan darare dama watan baki daya.
Ramadan Kareem.
via-the2brothers-links
Comments
Post a Comment