#Ramadan Kareem (1):
Alhamdulillah, Masha Allah
Ramadan Mubarak!
بسم الله الرحمن الرحيم
May Allah help us in standing (in prayer) and fasting in a manner that pleases Him, and may He count us all among the accepted and successful ones. Indeed, He is All-Hearing, Near, and Responsive to Supplications.
-INSHA ALLAHU YAU ZAMU LISSAFO MUKU LOKUTAN AMSAR ADDU'A.
-Amma Abin Lura Anan Shine Kowanne Lokaci Idan Mutum Yayi Addu'a, Allah Yana Ƙarɓa, Sai dai Ubangiji Cikin lkonsa da Falalarsa Ya Keɓanci Wasu Lokuta Ya Sanya Musu Albarka da Falala Fiye da Sauran Lokuta.
-Waɗannan Lokutan Sun Haɗa Da:
1. DAREN JUMA'A:
Wato Wato Ranar Alhamis da Dare, da Kuma Wunin Juma'ar. Manzon Allah (S) Yace: "Babu Wani Bawa Wanda Zai Dace Yana Addu'a A Cikinta Face Sai Allah Ya Amsa Masa".
2. WATAN RAMADAN:
"Gaba Ɗayansa Lokaci Ne na Amsar Addu'a.
3. DAREN LAILATUL QADARI:
"Shi ma Lokacin Amsar Addu'a Ne Sosai.
4. TSAKAR DARE:
Musamman ma Sulusin Ƙarshensa. Lokaci Ne da Allah Yake Gwanjon Rahamarsa Ga Bayinsa.
5. LOKACIN DA AKE ƘIRAN SALLAH, DA KUMA TSAKANIN ƘIRAN SALLAH DA TA DA IQAMAH.
6. LOKACIN DA AKA IDAR DA SALLOLIN FARILLAH.
7. LOKACIN DA AKA GAMA KARATUN ALQUR'ANI, KO WA'AZI KO WATA KOYARWA TA ILMIN ADDININ MUSULUNCI.
Shi ma Lokacin Ƙarɓar Addu'a Ne.
8. LOKACIN DA ZAKARA YA YI CARA:
Shi ma Lokacin Amsar Addu'a Ne.
9. LOKACIN TAFIYA TA ALHERI:
Kamar Tafiya Hajji, Sada Zumunci, Ziyara, Jihadi, Ko Fatauci. Shi ma Lokacin Amsar Addu'a.
10. RANAR ARFA:
"A Wannan Ranar, da Wanda Yake Makkah, da Wanda Yake Gida, Duk Allah Yana Amsar Addu'arsu.
11. LOKACIN SAUƘAR RUWAN SAMA:
Shi ma Ana Amsar Addu'a A Cikinsa.
12. LOKACIN DA AKA TSAI DA SAHUN YAƘIN ƊAUKAKA KALMAR ALLAH:
Shi ma Ana Amsar Addu'a Cikinsa.
13. LOKACIN DA MUTUM YAYI SUJADAH:
Shi ma Ana Amsar Addu'a A Cikinsa.
14. LOKACIN DA MUTUM YA FARKA DAGA BARCI:
Musamman Mutum Ya Karanta "Sub'hanallah Wal'hamdulillah, Wa la'ilaha'illal-Lah Wallahu Akbar (QAFA 10). Duk Abin da Ka Roƙa Mustajabah.
-Ya Allah Ka Biya Mana Dukkan Buƙatunmu Na Alkhairi Bihaƙƙi Muhammad Wa Ahli Muhammad.
via-the2brothers-links
Comments
Post a Comment