....Kafin Mutum Yayi Aure!
Bismillahir Rahmanir Rahim. Wata rana munje ziyara a gidan Babban Sufee, sai wani yayi tambaya akan babin Aure. To ga wasu daga cikin muhimman bayanai da yayi wanda na tsakuro na rubuta, ina fatan zasu amfanar. Gasu kamar haka: Aure ba soyayya ce kawai ba... nauyi ne, haƙuri ne, kuma ci gaba ne. Kafin ka nemi mutumin da ya dace... ka zama mutumin da ya dace tukunna. 💭 Alamomi 5 Da Ke Nuna Lallai Ka Shirya Yin Aure: 1. Kana tsoron Allah a ɓoye Ba a gaban mutane kawai ba... amma har a lokacin da babu wanda yake kallon ka. Domin asalin halayya ita ce wadda kake nuna wa a lokacin da Allah ne kaɗai yake kallon ka. 2. Kana iya ba da haƙuri cikin sauƙi Kana da niyyar ajiye girman kai a gefe. Domin aure ba zai iya dorewa ba a tsakanin mutane biyu da kowannensu yake son ya zama shi ne mai gaskiya a koda yaushe. 3. Ka fahimci matsayi (roles) ba tare da girman kai ba Shugabanci ba danniya ba ne. Mika wuya kuma ba rauni ba ne. Dukansu ayyuka ne na hidima... wadanda ake yin su domin Allah. 4...