....Kafin Mutum Yayi Aure!

  Bismillahir Rahmanir Rahim.

Wata rana munje ziyara a gidan Babban Sufee, sai wani yayi tambaya akan babin Aure. To ga wasu daga cikin muhimman bayanai da yayi wanda na tsakuro na rubuta, ina fatan zasu amfanar. Gasu kamar haka:



Aure ba soyayya ce kawai ba...

nauyi ne, haƙuri ne, kuma ci gaba ne.


Kafin ka nemi mutumin da ya dace...

ka zama mutumin da ya dace tukunna.


💭 Alamomi 5 Da Ke Nuna Lallai Ka Shirya Yin Aure:


1. Kana tsoron Allah a ɓoye

Ba a gaban mutane kawai ba...

amma har a lokacin da babu wanda yake kallon ka.

Domin asalin halayya ita ce wadda kake nuna wa

a lokacin da Allah ne kaɗai yake kallon ka.


2. Kana iya ba da haƙuri cikin sauƙi

Kana da niyyar ajiye girman kai a gefe.

Domin aure ba zai iya dorewa ba

a tsakanin mutane biyu da kowannensu yake son ya zama shi ne mai gaskiya a koda yaushe.


3. Ka fahimci matsayi (roles) ba tare da girman kai ba

Shugabanci ba danniya ba ne.

Mika wuya kuma ba rauni ba ne.

Dukansu ayyuka ne na hidima...

wadanda ake yin su domin Allah.


4. Kana iya jure wa son zuciya (gratification)

Ba ka gaggawa saboda matsin lamba daga mutane.

Ka fahimci cewa zaɓar abin da yake daidai...

ya fi zaɓar abu cikin sauri.


5. Ka cika mutum (whole) da kanka

Ba ka jiran wani ya zo ya gyara ka ba.


Kana da natsuwa...

yadda ba za ka ɗora wa abokin zamanka wani nauyi ba

wanda ba a halicce shi don ya ɗauka ba.


💭 TUNATARWA: 

Aure ba kammala ka yake yi ba... nuna wane ne kai yake yi.


🕊️ Yi aiki a kan kanka tukunna... Allah zai aiko maka da abin da ya dace.





-

-

KAFIN KA AURI MACE, KA TABBATA KA GWADA TA AKAN ABUBUWA 6.


Kafin ka amince da auren mace, ka tabbata ka gwada ta akan abubuwa shida (6) da zan lissafo. Idan ta fadi, ka san inda dare ya yi maka ka gudu kafin ka ruguza rayuwarka, Amma idan ta ci wannan jarrabawar, kayi duk iya kokarin da zaka yi domin ta zama matarka.


Su fa mata, wani lokacin fuskarsu daban, ainihin halinsu daban. Ga yadda zaka gwada ta:


NA FARKO:

Gwajin Talauci: Watarana ka kirata kace mata kasuwancinka ya ruguje ko an sace maka kudi, Yanzu baka kudi ko na Jari ne, baka da ko sisi a yanzu. Ka lura da kyau na kwanaki ko weeks kaga shin kulawarta zata ragu ko zata ci gaba da baka karfin gwiwa?


NA BIYU:

Gwajin Fushi: Ka dan bata mata rai da gangan a kan wani karamin abu. Ka lura da bakinta; shin tana zagi da cin mutunci idan ta fusata, ko tana kame kanta?


NA UKU:

Gwajin Rike Sirri: Ka fada mata wani babban sirri (na karya), ka nuna mata kar ta fada wa kowa. Idan kaji labari a wajen kawayenta ko danginta, ka san ba zata iya rufe maka asiri ba a gida.


NA HUDU:

Gwajin Biyayya: Watarana tana son zuwa wani waje da ta dade tana shiri, kawai ka nuna mata baka son zuwan nan. Idan ta yi mita ta fasa, tana da biyayya. Idan ta nuna maka kai baka isa ba, ka kiyaye..


NA BIYAR:

Gwajin Kwadayi: A maimakon ka sayi kyauta mai tsada, ka kawo mata karamar kyauta mara tsada sosai. Ka lura da fuskarta; masu godiya da karamin abu, su suke rike gida a lokacin babu.


NA SHIDA:

Gwajin Addini da Tarbiyya: Ka lura da yadda take ba wa sallah muhimmanci ba tare da ka matsa mata ba, sannan ka kalli yadda take mu'amala da na kasa da ita ko yara.


Ka sani shi aure rami ne da ba a fita. Da ka auri wasu matan a yanzu da ba su da tarbiyya, gaskiya gara ka mutu baka yi aure ba, ka zauna da kwanciyar hankalinka.




via-the2brothers-links. 

Comments

Popular posts from this blog

FULANI / FUL-FULDE

Wa Fatima! Wa Fatima!!

Recycler Virus