Ko Kasan A Wayarka Ta Hannu...

ABUBUWA GUDA 5 DA WATAQILA DAYAWANMU BAMUSAN WAYOYINMU NA TAFI DA GIDANKA SUNAYI BA

A yanayin neman taimakon gaggawa, wayar tafi-da-gidanka zata iya baka agaji ta kuma zamto silar ceton rayuwarka ko na waninka.

1. neman agajin gaggawa (Emergency Services) 🚑

Akwai number na Emergency duk duniya wanda kowacce wayar tafi-da-gidanka ka iya amfani dashi. Wannan number itace 112. Idan ka riski kanka a wajen da babu network, kuma ana buqatar taimakon gaggawa, kawai ka latsa 112 a lokacin. Wayarka zata searching dukkanin wani network dake wajen sannan ta baka emergency number da zaka kira. Wani abun burgewa ma shine koda wayar a kulle take da pattern ko pin, zaka iya latsa wannan emergency number din Wacce kyauta ake kira duk fadin duniya.

2. Shin makullin motarka ka manta ka kullesu acikin mota!

Idan ka kulle remote na motarka wanda baya dauke da key acikin motar kuma spare key yana gida, ka kira wani a gidan ta wayarsa da wayarka ta tafi-da-gidanka. Ka riqe wayar tafi-da-gidankan kamar dai-dai taqu daya daga jikin motar, saika umurci wanda ke gidan ya danna unlock button alhali yana riqe da remote din a daf karshen wayarshi ta daya bangaren da bai Kara kunneshi ba. Motarka zata budu. Idan kayi hakan ka ceci wani daga hawa Abin hawa ya kawo maka keys kuma kaima zaka saving lokacinka

3. Shin battery na wayarka ya zama empty ne?  Duk wayoyin battery power nasu sun 6oye? 📱

Domin dawo dasu, ka latsa  *3370#.. Ka aikata hakan yayinda wayar tana dafda daukewa domin rashin caji. Wayar taka zata restart ta wani hanya ta musamman na reserve inda zata nuna maka charging yakai 50%. Wannan reserve din zai kara charging kansa duk lokacin daka jona wayar taka a caji. Wannan sirrin yananan kusan a kowani manual na waya, sai dai dake muma manual ne muna tsallake karanta manuals na wayoyi muke amfani dasu.

4. Hana wayarka da'a ka sace amfani (Disabling)

Domin duba serial number na wayarka, ka latsa: (*#06#).

Nambobi guda 15 zasu bayyana a screen handset dinka. Ka rubuta ka ajiye a diary ko wani waje. Idan akasamu akasi wani yadauki aron wayarka ba tareda saninka ba (sacewa),  ka kira service provider naka ka basu code din. Zasu blocking wayar, bazata amfani wanda ya dauka ba, kuma idan kayi sa'a akwai tracker dazai locating a ina wanda ya sace wayar taka yake. Codes dinma sunanan a rubuce a jikin Kowani kwalin waya. Don haka ana adana kwalin waya idan an saya saboda tsaro.

5. Dawo da ATM PIN Number (Reversal)

Idan danfashi ko 6arawo yamaka matsin lamba akan sai Kunje ATM machine ka sanya pin dinka ka cire mar kudi, zaka iya sanar da police dake wajen ta hanya sanya pin naka na ATM a juye (misali 1234 ne pin din, sai ka sanya 4321 maimakon). Machine din zai iya baka kudin daka requesting, ammana nan take police zasu zo su shiga lamarin suyi ram da 6arawon. Kowani ATM machine yanada wannan emergency services din wanda dokace.

Ayi qoqarin yada irin wannan abu ga Yan'uwa da abokan arziki.

Comments

Popular posts from this blog

Dararen Lailatul Qadri:

£îd Mûbãräk

Taskar Ahlul Baitin-Nabiy (s).