Matasa, Dattawa da Tsoffi

*NASIHA ga waɗanda suka kai shekara 40 ko fiye da haka:*



1. Ka rinƙa yin *ƘAHO* sau ɗaya a shekara ko lafiyar ka lau.

2. Ka rinƙa *SHAN RUWA* ko da ba ka jin ƙishi, domin mafi girman abinda ke janyo taɓarɓarewar lafiya Shine: ƘARANCIN RUWA A JIKIN MUTUM.

3. Ka rinƙa *MOTSA JIKI* ko da yin Tafiya ne.

4. *KADA KA YAWAITA CIN ABINCI* ɗan madaidaici ya isar maka.

5. *KA RAGE YAWAN HAWA MOTA* Ka rinƙa tafiya da ƙafar ka zuwa masallaci ko wasu wurare na ziyara.

6. Ka daina *FUSHI* Ka daina barin damuwa a tare da kai domin hakan yana rage lafiyar mutum.

7. Kada ka rinƙa *YI MA KANKA DA IYALAN KA ROWA* ita dukiya an sanya ta ne *domin mu yi rayuwa da ita, ba wai domin muyi rayuwa saboda ita ba*

8. Kada ka *MATSA MA KANKA* ga abinda baka da ikon tabbatar da shi, ko wanda baka iya mallakar sa, *Ka rinƙa mancewa da irin waɗannan*

9. Ka rinƙa *TAWALU'U* da kuɗi da girma da matsayi dukkan su *Girman kai* yana shiga cikin su. Kada ka rinƙa nuna isa akai. *Mai ƙanƙan da kai mutane suna ƙaunar sa, kuma Allah ya na ɗaga darajar sa*

10. Idan ka ga ka fara *HURHURA* Ba hakan yana nuna mutuwa tazo maka bane, abinda yafi a gare ka: *Ka dage da Ambaton Allah, kuma ka ci gaba da jin daɗin rayuwar ka da Halal*.

11. *KADA KA YAWAITA HIRAR DARE, KA RINƘA BACCI DA WURI*

12. Kada ko da wasa ka bar *SALLAH* domin itace Ribar ka a nan duniya da kuma Lahira.

To sai Kuma matasa, su kula da wadannan "five rules, for better life" dake a hoton kasa.


Comments

Popular posts from this blog

Dararen Lailatul Qadri:

£îd Mûbãräk

Taskar Ahlul Baitin-Nabiy (s).