Taskar Ahlul Baitin-Nabiy (s).
☆via-the2brothers-links☆ Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai. Imam Ali (A.S) Yana cewa: "Ka tsare harshenka kamar yadda kake tsare dukiyarka. Domin sau da yawa wata maganar tana kore alheri. Wata maganar kuma tana janyo sharri". Imam Ali (A.S) Yana cewa: "Babbar hanyar zama lafiya itace sallamawa ga iko da kaddarar ubangiji". Imam Ali (A.S) Yana cewa: "Jure masifa jarumta ce kamun kai arzikine. Tsare kai daga sabon Allah shine babbar garkuwa". Imam Ali (A.S) Yana cewa: "Talauci yana nakasa hujjar ma'abocin hankali. Talaka yakan zama bako a garin haihuwarsa." Imam Ali (A.S) Yana cewa: "Kada kaji kunya ko nauyin bayar da kadan. Domin hana kadan din yafi bayar da kadan din karanta. Imam Ali (A.S) Yana cewa: "Mai aikata kyakkyawan aiki yafi kyakkyawan aikin kyau kamar yadda mai aikata mummunan aiki yafi mummunan aikin muni". Imam Ali (A.S) Yana cewa: "Lafiyar jikinka tana karuwa idan hassadarka tana raguwa". I...