Taskar Ahlul baitin-Nabiy (s)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

📜 دعاء الفرج


”إلـهي عَظُمَ الْبَلاءَ، وَبَرِحَ الْخَفاءُ، وَانْكَشَفَ الْغِطاءُ، وَانْقَطَعَ الرَّجاءُ، وَضاقَتِ الأرض، وَمُنِعَتِ السَّماءُ، واَنْتَ الْمُسْتَعانُ، وَاِلَيْكَ الْمُشْتَكى، وَعَلَيْكَ الْمُعَوَّلُ فِي الشِّدَّةِ والرَّخاءِ، اَللّـهُمَّ صَلِّ عَلى مُحَمَّد وَآلِ مُحَمَّد، اُولِي الأمر الَّذينَ فَرَضْتَ عَلَيْنا طاعَتَهُمْ، وَعَرَّفْتَنا بِذلِكَ مَنْزِلَتَهُمْ، فَفَرِّجْ عَنا بِحَقِّهِمْ فَرَجاً عاجِلًا قَريبًا كَلَمْحِ الْبَصَرِ اَوْ هُوَ اَقْرَبُ، يا مُحَمَّدُ يا عَلِيُّ يا عَلِيُّ يا مُحَمَّدُ اِكْفِياني فَاِنَّكُما كافِيانِ، وَانْصُراني فَاِنَّكُما ناصِرانِ، يا مَوْلانا يا صاحِبَ الزَّمانِ، الْغَوْثَ الْغَوْثَ الْغَوْثَ، اَدْرِكْني اَدْرِكْني اَدْرِكْني، السّاعَةَ السّاعَةَ السّاعَةَ، الْعَجَلَ الْعَجَلَ الْعَجَل، يا اَرْحَمَ الرّاحِمينَ، بِحَقِّ مُحَمَّد وَآلِهِ الطّاهِرينَ.“


• مفاتيح الجنان

 Wasu Daga Cikin Zantuka/Hadisai Na Imam Mahdi (Ajjalallahu Ta'ala Farjahu):




1. Al-Imamul Mahdi (a.f)  yana cewa: 


"Hakika a Aljanna Mata ba Su daukar Ciki, kuma ba Su haihuwa, idan Mumini ya yi Sha'awar samun Da, Allah zai halitta masa Shi ne ba tare da daukar ciki ko haihuwa ba,  akan surar da yake so Dan ya kasance, kamar yanda ya halicci Adamu a matsayin aya". 


-Littafin Biharul anwar juzu'i na 53 shafi na 163 hadisi na 4.




2. Al-Imamul Hujja (a.f)  yana cewa: 


"Yana daga Falalar Allah swt cewa hakika Mutum ya kan manta Tasbihi alhali yana jujjuya Carbinsa,  sai Allah ya rubuta masa (Ladan) tasbihi".


-Littafin Biharul anwar juzu'i na 53 Shafi na 165 hadisi na 4.




3. An samo daga Sahibul Asri waz-Zaman (a.f)  ya ce: 


"Kuna so in yi muku bushara dangane da Atishawa? (Mai ruwaya ya ce)  sai na ce haka ne ya Maulana. Sai ya ce da Ni: Ai aminci ce daga Mutuwa har tsawon kwana uku".


 -Littafin Wasa'ilus-Shi'a juzu'i na 12 shafi na 89 hadisi mai lamba 15717.

.


4. Ansamo daga Limamin wannan Zamanin (a.f) yana cewa: 


"Hakika babu dangantaka a tsakanin Allah da wani Mutum,  kuma duk wanda ya yi inkari na, ba shi tare da Ni, Halanyarsa za ta zama irin hanyar Dan Annabi Nuhu ne". 


-Littafin Biharul anwar Juzu'i na 50 shafi na  227 hadisi na 1.



5. Al-Imamul Muntazar (a.f)  yana cewa: 


"Shin ba Ku san cewa hakika Kasa ba ta wofinta daga Hujjar Allah ba, ko dai ya kasance a Zahiri ko kuma ya kasance a cikin fakuwa?". 


-Littafin Biharul anwar juzu'i na 53 Shafi na 191 hadisi na 19.



Akwai ci gaba insha Allah.


          ☆via-the2brothers-links☆

Comments

Popular posts from this blog

Dararen Lailatul Qadri:

£îd Mûbãräk

Keyboard Shortcut