Recycler Virus
RECYCLER VIRUS – Shi ke cinye Folder ya mayar da ita SHORTCUT A KWAMFUTA. RECYCLER VIRUS Recycler Virus wani daya daga cikin virus ne da ake da su a cikin kusan Virus sama da miliyan bakwai da ake da su a duniya, na san wani zai yi mamaki a kan haka, shi dai makasudin yin wannan virus domin ya rinka hayayyafar kan shi a cikin computer ne, ta yadda zai rinka kirkirar folder da take cikin computer ka. Misali idan wannan virus ya shiga cikin Kwamfutarka kuma babu antivirus a cikin ta zai rinka kirkirar sunan folder yana karawa a cikin folder da ka bude. misali idan ka shiga cikin My Music folder sai ka ga wata irinta da suna My Music ammakarshen zai kare da .exe. Wani yanki na cutarwa da wannan Virus yake yi shi ne zai iya share maka file ko kuma document da ke cikin computer su koma da .exe idan haka kuwa ta faru idan antivirus ya gansu zai sharesu. Bayan da aka gano yadda wannan cutarwar take sai suka canza salo ta yadda idan wannan virus ya kama computer ka ba zai cinye files d...