Dararen Lailatul Qadri:
Alhamdulillah yau Allah ya kawo mu dare na farko (cikin dararen lailatul Qadri) a wannan wata mai tarin Albarka. LAILATUL KADARI YA FI DARE DUBU (1000) A cikin watan (Ramadan) akwai wani dare ya fi dare 1000. Wato ka samu ka yi ibada a cikinsa ya fi ka yi dare dubu kana ibada kenan. Wato kimanin shekaru kusan 100, wajen tis'in da nawa kenan? An ce 'Khairun' ne, ba a ce daidai wadaida ba. اللهم صل على محمد وآل محمد وعجل فرجهم📿 SALLAR DAREN SHA TARA GA WATAN RAMADAN, DAREN LAILATUL QADRI. Yau Alhamis18 ga Watan Ramadan dare na Farko daga cikin dararen lailatul Qadri Wato Daren 19,21,23, Wadan nan Sune dare na lailatul Qadri . AYYUKAN DAREN YAU 19 GA WATAN RAMADAN 1. Anaso ayi Wanka irin na ibada a Daren Yau, Kuma Anfiso Ayishi a Farkon Daren. 2. Karanta Ziyarar Imam Hussain (As) Tana daga cikin Ayyuka mafi girma a wannan dare. 3. Tsinewa Makashin Wasiyin Manzon Allah (Imam Ali As) sau 100 "Allahumma la'an Man Qatala Amirul Muminin kafa 100. 4....