Taskar Ahlul Baitin-Nabiy (s).
☆via-the2brothers-links☆ Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai. -HADISAI GOMA DAGA IMAM BAQIR (AS): 1- Imam Baqir (AS) Yace: "Farkon Abin da Za'a Yiwa Bawa Hisabi Dashi Itace Sallah, Idan ta Ƙarɓu to Dukkan Sauran Ayyukan Bawa Za'a Karbe su. - Bihar 7/267. 2- Imam Baqir (AS) Yace: "Hadisan mu (Maganganunmu) Suna Raya Zukata Ne". - Bihar 2/144. 3- Imam Baqir (AS) Yace: "Duk Wanda Ya Kasance Mai Biyayya ga Allah (T) to shi Masoyinmu Ne. Hakanan Kuma Wanda Ya Kasance Mai Saɓawa Allah to Shi Maƙiyinmu Ne." - Alkafiy 2/75. 4- Imam Baqir (AS) Yace: "Ku Nemi ilimi, Domin Nemansa Abu ne Mai Kyau Kuma Koyonsa Ibada Ce." - Biharul Anwar 74/189. 5- Imam Baqir (AS) Yace: "Me Tuba Daga Zunubai Kamar Wanda Bashi da Zunubai Ne Kwata-Kwata" - Wasa'il 16/74. 6- Imam Baqir (AS) Yace: "Ya Wajaba ga Mumini Akan Ɗan Uwansa Mumini Ya Ɓoye (Sirranta) Masa Manya Manyan Zunubansa Guda Saba'in (70) Daga Sanin Mutane." - Bihar 7...